Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun Daukaka Kara A Gambia Ya Bada Umurnin Sakin Fursinonin Siyasa


Adama Barrow, sabon shugaban Gambia mai jiran gado
Adama Barrow, sabon shugaban Gambia mai jiran gado

Kwannaki kadan bayanda aka kada shugaban kasar Gambia, Yahya Jammeh a zaben da aka yi a kasarshi, wata kotun daukaka kara a kasar ta bada umurnin a saki wani babban jigon ‘yan adawa tareda wasu fursunonin siyasa su 18 da aka tsare.

Madugun ‘yan adawar mai suna Ousainou Darboe da sauran ‘yan jam’iyyar adawa ta U-D-P dai an yanke musu hukuncin daurin shekaru ukku-ukku ne a watan Yulin da ya gabata, bayanda aka kama su cikin wata zanga-zangar siyasa ta lumana, inda suke neman a yi sauye-sauye ga dokokin zabe na Gambia.

Shugaban Gambia Yahya Jammeh wanda ya sha kaye
Shugaban Gambia Yahya Jammeh wanda ya sha kaye

Ganin abinda ya faru, yanzu haka wata jam’iyyar adawa ta Gambia ta fito tana kira da a saki daukacin sauran dukkan fursunonin siyasan dake tsare a kasar.

Saihou Mballow, daya daga cikin jagabannin jam’iyyar G-D-C dake da rassa a kasashen waje yayi kira akan kungiyoyin kare hakkin jama’a irinsu Amnesty International da Human Rights Watch da su sa hannun don sako sauran mutanen da aka tsare a bisa dalilan siyasa.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG