Tawagar shugabannin kasashen Afirka ta Yamma wadanda suka hada da Ghana da Laberiya da Saliyo da kuma Guinea, ta dauki wannan mataki na yin sulhu da tattaunawa a dai dai lokacin da kasashen duniya da kungiyoyi daban daban har Majalisar Dinkin Duniya, wadda ke yin tur da Allah wadai da wannan yunkuri na shugaba Jameh.
A wata sanarwa da ta fito daga fadar Shugaba Mohammadu Buhari, tace shugaba Buhari ya hade da sauran shugabannin domin yin tattaunawa da Yahaya Jammeh da kuma sabon shugaban da aka zaba mai jiran gado Adama Barrow, dangane da matakan da suka kamata shugabannin biyu su dauka, na tabbatar da an samar da zaman lafiya an kuma mika mulki ga farar hula ba tare da tashin hankali ba.
Mai sharhi kan al’amuran kasa da kasa ambasada Lawal Munnir Mohammed, yace lalle wannan ziyara da wannan shugabannin suka kai zatayi muhimmanci ganin cewa kusan da yawansu sun dandana irin abubuwan da Yahya Jammeh yake ciki, kuma za a iya yin sulhu ko yarjejeniya don tabbatar da an mika mulki ba tare da an ciyar da kasar baya ba.
Domin karin bayani.