Shugaban kungiyar Kwamred Ayuba Wappa ya bayyana abubuwan da kungiyar ta shirya zata yi.
Yace akwai gangami da zasu yi ranar 10 ga watan nan wanda yake da nasaba da kyakyawan shugabanci da suke bukata daga shugabannin kasar. Suna son
'yan siyasa su yi la'akari da shugabanci mai adalci saboda a shekarun baya an yi rashin kyakyawan shugabanci. Mutane a lokacin sun sha yin sama da fadi da dukiyar jama'a. Sun sace kudade masu dimbin yawa, kimanin wajen biliyan dari da hamsin dalar Amurka.
Yawan sace sace ya sa ba'a iya biyan albashi ba ko kudin fansho. Cin hanci da rashawa ya bar asibitocin kasar babu magani, shi ne kuma ya jefa kasar cikin halin kakanikayi.
Kungiyar na shirin gangamin ne a duk jihohin Najeriya da Abuja. Kungiyar ta bada umurni kowace jiha ta shirya yin gangamin goyon bayan yaki da cin hanci da rashawa. Duk wanda aka sameshi da cin hanci da rashawa a tona asirinsa, kada ayi masa rufa rufa.
Ga rahoton Hssan Maina Kaina.