Tshohon dan majalisar dokoki daga jihar Adamawa kuma masani kan harkokin diflomasiya Ibrahim Abdulmunmuni Song yace banda shugaba Murtala Muhammad da shugaba Obasanjo lokacin da yake soji babu wani shugaban kasa da ya farfado da kiman Njeriya a idanun duniya kamar shugaba Buhari cikin kwanaki dari akan mulki.
Shugaba Buhari ya yi nasarar sake farfado da martaba da kuma darajar Najeriya saboda irin hadin kan da ya samu daga kasashen ketare wadanda a da sun guji kasar. Kasashen sun bada hadin kai wajen maido da dukiyar kasa da aka sace aka buye a bankunan kasashen duniya.
Inji Abdulmunmuni Song kudaden da aka dawo dasu da wadanda aka rubuta wasika za'a dawo dasu da wasu da suka mika kansu sun isa su biya albashin ma'aikatan kasar na shekaru bakwai. Kafin Buhari ya hau mulki wasu suna barin kasar. Amma yanzu kasar China ta dawo da Indiya da Jamus. Kowace kasa yanzu tana son ta dawo ta cigaba da harkokinta a Najeriya.
Shugaba Buhari cikin kwanaki dari ya kusa kawo karshen rikicin Boko Haram.
Barrister Abubakar Usman mai sharhi akan harkokin kasa da kasa yace ziyarar da shugaba Buhari ya kai kasashen dake makwaftaka da kasarsa ba zai rasa nasaba ba irin fahimtar da ya yiwa rikicin Boko Haram ba. Ya gane matsala ce dake bukatar hadin kan kasashen. A cewarsa kwalliya ta soma biyan kudin sabulu.
Matakan da shugaba Buhari ya dauka na murkushe Boko Haram sun karfafa gwiwar kasashen duniya na maido da huldar kasuwanci da Najeriya. Halartar taron kasashen G7 da shugaban ya yi ya taimaka kwarai.
Ga karin bayani.