To sai dai kwararru a fannin zamantakewar dan Adam na ganin Kungiyar Kwadagon tana yajin aikin ne don gashin kanta, ba don talaka ba.
Wata sanarwa mai dauke da sa hannun mataimakin babban sakataren Kungiyar Kwadago Christopher Onyeka, na cewa sanarwar da kungiyar ta ba gwamnatin tarraya a ranar daya ga wannan wata na Satumba da muke ciki, tana dauke ne da wa'adin kwanaki 21 wanda har yanzu wa'adin bai kare ba.
Kungiyar ta ce za ta iya tilastawa ma'aikatu da hukumomin kasar daukar matakin shiga yajin aikin sai baba ta gani, idan har ba a biya mata bukatun ta ba.
Idan ba amanta ba, don nuna muhimmancin wannan wa'adi da ta bayar ne kungiyar ta gudanar da yajin aikin gargadi na kwanaki biyu a ranakun 5 da 6 na wannan watan, inda aka dakatar da ayyukan zamantakewa da tattalin arziki a jihohi da dama, tare da rufe bankuna, ma'aikatun bada wutar lantarki da hukumomi da sassan jama'a a wasu jihohi.
Comrade Nasir Kabir, Sakataren tsare-tsare na Kungiyar Kwadago, ya ce in gwanatin Tinubu da gaske ta ke, ta yi maza ta nemo kudi na kawo wa ‘yan kasa tallafi kan matakin tsadar man fetur da al'umma ke fama da shi.
Nasir ya ce kasa tana da kudi da ya kamata ta biya ma'aikata dubu 300 a wata, ko dubu dari 400, saboda haka Kungiyar Kwadago ba za ta yarda da wata yaudara ba.
Amma ga shugaban Muryar Talaka na Damaturu a jihar Yobe Saleh Bakoro Sabon Fegi, yana mai cewa Kungiyar Kwadago ta rinka jinjina batun yajin aikin da ta ke yawan yi. Saleh ya ce yana so kungiyar kwadago ta sani cewa ita ce kungiyar da ya kamata ta samar wa ‘yan kasa 'yancinsu ko ta nema masu sauki daga wurin gwamnati amma kuma ba a nan gizo ta ke saka ba.
Saleh ya ce Kungiyar Kwadago ba ta bayyana wa al'umma bayani idan sun gana da gwamnati, domin ana ta yajin aiki amma ba a samun ci gaba. Saleh ya kuma ce idan kungiyar kwadago ba ta yi a hankali ba, wata rana ma za ta kira yajin aikin babu wanda zai fito.
Shi ma kwararre a fannin zamantekawar dan Adam kuma mai nazari a al'amuran yau da kullum, Abubakar Aliyu Umar ya ce Kungiyar Kwadago ta duba yadda talakawa suke wahala idan an shiga yajin aiki. Abubakar ya ce idan Kungiyar Kwadago ba ta tsaya da gaskiya ba, za a daina girmama yunkurin kiran a shiga yajin aiki.
Kungiyar Kwadago ta ce matakin da gwamnati ta dauka na bai wa ‘yan Majalisa Naira biliyan 70 sannan ko wannen su ya samu sama da Naira miliyan 100 a kasar da mutane miliyan 137 ke fama da talauci, ba abu ne da kungiyar za ta kau da ido akai ba.
Sai dai nan take fadar shugaban Najeriya ba ta ce komai ba.
Saurari cikakken rahoto daga Medina Dauda:
Dandalin Mu Tattauna