Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Fattataki 'Yan Ta'adda a Bauci


Kwamishinan 'Yan Sanda na Jihar Bauci, Mohammed Ladan.
Kwamishinan 'Yan Sanda na Jihar Bauci, Mohammed Ladan.

Jami’an tsaro a jihar Bauci sun yi nasaran fatattakan wasu ‘yan bindiga wadanda suka kai hari kamfanin Mother Cat dake garin Yana cikin karamar hukumar Shira a jihar Bauci mallakar ‘yan kasan Lebanon.

Shi dai kamfanin Mother Cat yana aikin farfasa duwatsu ne inda ‘yan bindigan suka je suka kwashi sinadarai da ake amfani dasu wajen hada boma-bomai.

Malam Musa Muhammad Mai Almajirai shine shugaban masu gadin kamfanin, yace “abunda yake faruwa jiya tun karmar karfe daya da rabi na dare akwai wasu ‘yan bindiga suka shigo mana yadi suka samu masu gadi na mutu biyu suka ritsa su,suka ce su nuna masu inda ake aje kayan nakiya wanda ake fasa dutse dashi suka ce basu san ida ake ajewa ba suka yi masu burga haka su masu gadi na sun ga Hilux kuda uku da machina hudu ko biyar,amma yawan mutane sun kai mutum talatin.”

Kakakin hukumar ‘yan sandar jihar DSP Haruna Muhammad yace ”da muka sami bayani sai jami’an tsaro suka garzaya suka yi bata kashi da wadannan mutane na kusan awa daya, daga bisani mutanen suka yarda wannan mota daka dauke da wannan ababen fashewa din da wasu baburansu suka gudu.”

'Yan Ta'adda Sun Kai Harin Neman Sinadarin Bom - 3'03"
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG