Kwamishanan ilimi na jihar Musa Inuwa Kubo shi ya tabbatar wa Muryar Amurka hakan. Kwamishanan ya tabbatar da hakan bayan ya kai ziyarar gani da idanunsa zuwa garin Chibok inda lamarin ya faru. Amma yace ba zai iya tabbatar ko karyata sanarwar da sojoji suka fitar a Abuja ba. Yace mai yiwuwa sun samu kubutar da daliban ne amma su a jihar Borno basu da wannan tabbacin.
Shekaranjiya ne sojoji suka fitar da sanarwa cewa sun kubutar da yawancin yaran saura guda takwas kawai. A kan wannan ikirarin na sojoji kwamisahanan yace baya son su samu sabani da juna. Yace tana yiwuwa daliban na wurin su sojoji. Yace shi da jama'ar Chibok da shugabar makarantar da iyayensu suna nan suna jira sojoji su kawo masu daliban da suka kubutar.
Daya daga cikin iyayen dake garin Chibok yace ba gaskiya ba ne cewa an kubutar da yawancin yaran. Yace maimakon hakan 'yan gora da wasu mafarauta sun kama hanyar dajin da 'yan Boko Haram suka kafa sansani.
Ga rahoton Haruna Dada Biu.