Kwamitin tsaro a majalisar dokokin kasar Niger ya samu bakunci wata tawagar ‘yan majalisar dokokin FARANSA a ci gaba da neman hanyoyin magance matsalolin ta’addanci da na bakin haure a wannan lokaci da satar mutane don neman kudin fansa ke kokarin samun gindin zama a kasashen Sahel.
Dan majlisa HAMA ASA ya bayyana cewa "mun yi mahawara da takwarorinmu na FARANSA inda muka ganar da su cewa kasar Niger na matsayin wani dungalin dake kare kasashen turai daga barazanar ‘yan ta’adda sai dai sabon salon da wannan yaki ke bijirowa da su a halin yanzu na nunin akwai bukatar kasashen turai su tallafawa kasashenmu domin idan aka duba kudaden da ya kamata a saka a fannonin jin dadin rayuwar jama’a ne ake sayen kayan yaki da su".
A karshen wannan zama ‘yan majalisar na FARANSA sun yi alkawalin isarda wannan sako zuwa ga takwarorinsu na gida da na sauran kasashen turai. Asa ya ce sun yanke shawarar sake gudanar da makamancin wannan taro a watan Disamba mai zuwa a FARANSA domin ci gaban abubuwan da suka zanta a kansu a taron Yamai .
Ta hanyar wannan yunkurin hadin gwuiwa ‘yan majalisar dokokin Niger da takwarorinsu na FARANSA na fatan shawo kan Majalisar Dinkin Duniya, MDD, ta saka rundunar hadin gwuiwar G5 SAHEL a karkashin kudirinta na 7 don ganin ta kaddamar da ayyukanta gadan gadan.
A saurari rahoton Souley Barma
Facebook Forum