Ya kara da cewa tankokin daukan mai an yi sune don daukan mai daga defo zuwa gidajen mai.
Amma yanzu sai jigila su keyi na daukan mai daga Legas zuwa sassa daban-daban na kasa, wanda haka dole ne ya kawo jinkiri.
Shugaban yace babu yanda za'a maida tankokin daukar mai su zama tamkar layin bututun mai da ake amfani dashi wajen turo mai zuwa defo-defo.