Yayin da Najeriya ke cigaba da gudanar da shirye-shiryen zaben shekarar 2023 mai zuwa, wani abun jan hankali a jerin masu tsayawa takara shi ne yadda ake samun karin mata da ke fitowa domin a dama da su musamman wajen samun manyan mukamai.
Tambayar ita ce, shin matan sun shirya kai Najeriya tudun mun tsira la'akari da tarin matsalolin daya addabi kasar?
Kwararriya a fannin bada shawarwari ta kasa da kasa kana shugabar wata kungiya mai suna INCREASE dake rajin kare hakki, lafiyar mata da matasa daga Jihar Neja, Dorothy Nuhu-Aken’ ova, na daga cikin matan da suka bayyana aniyarsu ta tsayawa takarar shugabancin Najeriya a zaben shekarar 2023 da ke tafe karkashin inuwar jam’iyyar SDP mai alamar Doki, duk da tarin matsalolin da Najeriya ke ciki, Dorathy ta bayyana cewa zata iya kawo canji a kasar idan ta samu damar jagorantar kasar tun da maza sun gaza a fagen siyasa kuma kamata ya yi su bada hanya ga mata su gwada tasu baiwar da basira ta jagorancin kasar
Ko da yake dai Gwamnatin Najeriya ta bi sawun wasu kasashe wajen inganta tsarin da ta ke da shi ta hanyar jagorantar wani sabon shiri ga mata a kasar don ganin sun shiga harkokin siyasa dumu-dumu gabanin babban zaben 2023, masanin kimiyar siyasa a Najeriyar, Dakta Faruk BB faruk ya bayyana cewa mata sun rike kasashe da dama cikin amana
To sai dai a cewar 'yar fafutuka a kasar Ummulkhairi Abdulmunini Iliyasu, daya daga cikin kalubalen da ake fuskanata shi ne rashin samun goyon bayan mata idan suka ga yar’uwarsu mace ta fito takarar shugabanci ko neman wani mukami a kasar.
Kididdiga ya nuna cewa mafi karancin matsayi da mukamai da mata ke samu a Najeriya har yanzu yana kan kashi 6.7 cikin dari, adadin da yayi kasa sosai idan aka kwatanta da adadin kasashen duniya na kashi 22.5 cikin dari, inda nahiyar Afurka ke da kashi 23.4, sai kuma yankin yammacin Afruka dake da kashi 15.
Saurari cikakken bayani cikin rahoton Shamsiyya Hamza Ibrahim