Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mun Yi Tir Da Tabarbarewar Tsaro; Amma Ba Mu Ce Buhari Ya Sauka Ba - JNI


Muhammadu Buhari
Muhammadu Buhari

Jama’atu Nasril Islam (JNI) ta yi Allah wadai da tabarbarewar tsaro a Najeriya; amma ta karyata rahotannin da ke cewa ta ce Shugaba Buhari bai cancanci cigaba da shugabancin Najeriya ba. Da ta ke bayani ta bakin Babban Sakatarenta, Dakta Khalid Aliyu, JNI ta ce abin da ta ce a sanarwarta, wadda shi Dr Khalid ya rattaba wa hannu shi ne ta na mai bayyana rashin jin dadinta saboda radadin yanayin rashin tsaro a kasar ke haddasawa, ta na mai kiran da hukumomi su tashi haikan wajen daukar matakan da su ka dace. JNI ta ce ta ko ina ka duba yanayin tsaro ya sukurkuce: Kama daga zubar da jinni, zuwa sace sacen mutane sa sauran tashe tashen hankula da ake fama da su a kasar.

JNI ta ce Allah ya dora ma gwamnatin Najeriya nauyin tabbatar da tsaro a kasar. “Ita gwamnati ta tashi, wannan wajibi, ita Allah ya dora wa. Batun tsaro dai ba wani mutumin da zai iya zuwa ya ce zai tinkari harkar tsaro sai ita gwamnati da yake dama wannan wajibinta ne kuma aikinta ne. “ Dakta Khalid ya kara da cewa, “Kodayake ta na kokarinta matukar iyawa, to amma dai akwai bukatar ta kara himma; ta kara himma har sai tsaro ya dawo al’umma ta zauna lafiya ana harkoki da tafiye tafiya ba cikin halin dar dar ba; ba a cikin halin barazana ba.”

JNI ta ce a duk duniya, muddun gwamnati ta kasa wajen tabbatar da tsaro to “kasancewarta a matsayin gwamnati akwai damuwa. Wannan shi ne abin da mu ka fada. Babu wani wanda ya kira sunan Shugaban kasa ya ce shi bai kamata ba. Wanda ya ke so ya jefi shugaban kasa da magana to sai ya jefe shi da bakinsa ya ce Shugaban kasa ya tashi ya tafi – wannan kuma ya zama fassararsa kenan – idan abin da yak e son cewa kenan – sai ya je ya rubuta irin na shi. Amma mu dai ba abin da mu ka rubuta ba kenan.”

Da ya ke amsa tambaya, Dakta Khalid ya ce idan aka ce Shugaban kasa ya tafi “to shikenan sai kasar ta zama babu shugaba kenan? Ai wani rikicin ne kuma zai sake dawowa. Don haka ba wannan bayanin aka yi ba”

Saurari cikakken rahoton Umar Faruk Musa cikin sauti:

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG