Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Boko Haram Ta Balle gida Biyu


Yanzu dai ya tabbata cewa bangaren Boko haram na Malam Mammannur, sun balle daga uwar kungiyar ta Boko haram dake karkashin jagorancin imam Abubakar Shekau.

A cikin wani faifai da sashen Hausa na muryar Amurka ta samu a daren jiya, malam Mammannur ya zargi Abubakar Shekau da kashe kashen rayukan mutane ba bisa hakki ba.

Mammannur ya koka da yadda Shekau ke ci gaba da kashe manyan kwamandojin kungiyar.

A cikin faifan mai kusan tsawon sa’a guda da rabi, daya daga cikin manyan kwamandojin da suka balle Imam Abu Fatima ya ce ya za’ayi suke gugu kuma basa samun nasara kan abokan gabar su?

Saurari cikakken rahoton Hassan Maina Kaina.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:58 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG