Mataimakin shugaban jami'ar Najeriya da Turkiya dake Abuja Farfasa Husseini Sad ya nuna rashin jin dadinsa dangane da kiran da jakadan Turkiya dake Najeriya ya yi na cewa a rufe duk makarantun turkawa dake Najeriya.
Yace makarantun na Najeriya ne domin suna bin dokokin kasar sau da kafa. Yace ma'aikatar ilimi da hukumar dake kula da jami'o'i sun gamsu da abun da suke yi.
Jami'arsu ta kasa da kasa ce tare da kawo malamai daga koina daban daban. Yace tun shekarar 2009 suke aiki tukuru babu kama hannun yaro.
Suleiman Obadiah mataimakin shugaban editocin Najeriya yana da 'ya'ya a jami'ar. Yace a tsawon shekaru da 'ya'yansa suka yi suna daukan karatu shi bai ga wani abun asha da suka yi ba. Yace makarantun suna aikin alheri. Sun dauki 'yan Najeriya fiye da dubu biyu aiki.
Yace su yi siyasarsu a can kada su kawota Najeriya. Makarantun akwaisu a kasashe dari da wan abu babu dalibinsu daya da aka taba kamawa da laifin asha. ko kuma aka samesu suna da alaka da kungiyar ta'adanci.
Ga rahoton Hassan Kaina Mana da karin bayani.