Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwamitin Binciken Rikicin 'Yan Shi'a Da Soji Ya Ce Mutane 348 Ne Suka Rasu


Kwamitin binciken da gwamnatin jihar Kaduna a arewacin Najeriya ta kafa, ya ruwaito cewa mutane 348 ne ‘yan kungiyar Shi'a, sojoji suka kashe biyo bayan wani cece kuce daya shiga tsakanin su a cikin watan Disambar bara.

Sai dai wakilin Amurka dake babban birnin tarayyar Najeriya Chika Oduah yace biyo bayan fidda wannan rahoton da kwamitin yayi cikin wannan satin, yasa jama'ar kasa na tofin ALLAH waddarai ga ‘yan kungiyar ta Yan Shi'a.

Shi dai wannan kwamitin binciken da gwamnatin jihar Kaduna ta kafa ya samu sojoji da laifin wuce makadi da rawa wajen anfani da ikon su akan ‘yan kungiyar ta Shi'a, lokacin da cacar baki ta kaure tsakanin sojojin da ‘yan shi'a akan hanya, watanni 8 da suka gabata.

kwamitin ya jaddada cewa mutane 348 ne na kungiyar ta ‘yan shi'a suka mutu da soja guda sakamakon wannan hatsaniyar.

Suma kungiyoyi kare hakkin bil adama na kasa da kasa sun fidda kwatankwacin irin wannan rahoton.

Amma rahoton kwamitin na jihar Kaduna ya danganta mafi rinjayen laifin ga kungiyar ta ‘yan Shi'a abinda mai Magana da yawun rundunar sojojin Kasar Kanar Sani Usman ya jaddada.

Sai dai kuma Kanar din yaki yace uffan game game da shawarar da kwamitin na jihar Kaduna ya bayar na cewa a gurfanad da duk wani sojan da aka samu da laifi cikin wannan al’amari na kashe fararen hula har su 348.

Kwamitin yace kungiyar ce ta ingiza ‘ya’yanta suka bijirewa doka.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG