John Mahama dake kan karagar Mulki a yanzu na neman zama shugaban kasa karo na biyu in da yake takara da shugaban yan adawa Nana Akufo-Addo, wanda ya kwada da kasa a zaben shekaru hudu da suka wuce.
Akufo-Addo, Tsohon ministan Harkokin waje yayi amfani da yanayin da tattalin arzikin kasar Ghana ke ciki domin yin kamfe, inda yake kalubalantar Mahama da Jam’iyyarsa ta National Democratic Congress da rashin cancanta.
Ghana na daya daga cikin manyan kasashen da ke fitar da Mai da Koko da kuma Gwal. Amma Mulkin Mahama na farko ya sami tangarda da faduwar farashin mai a duniya, wanda ya jawo tashin farashin kayayyaki.
Gwamnatin kasar Ghana ta karbi bashin kudi kimanin dalar Amurka 918 daga Hukumar Lamuni Ta Duniya (IMF). Shugaban kasa ya kewaya kasar a lokutan Kamfe domin tallata sabbin hanyoyin da kuma yadda zai aiwatar da aiyukansa.
Ghana dai ta kasance kasar da taci moriyar Demokradiyya a Nahiyar Afirka, Amma kamfe na wannna shekarar ya fito da barazanar tsoratar da Masu zabe da kuma damuwa akan Ma’aikatar Zabe ta kasar.