Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Kwamitin Tsaro Na Kasashen Sahel Sun Fara Taro A Nijar


Ministan Cikin Gidan Nijar Bazoum Mohamed
Ministan Cikin Gidan Nijar Bazoum Mohamed

Shugabannin ma’aikatun tsaro da samar da bayanan sirri daga kasashe takwas na yankin SAHEL da SAHARA mambobin kungiyar UFL sun fara gudanar da wani taro a jamhuriyar Nijar, yayin da kungiyar mai alhakin tattarawa da musanyar bayanai a tsakanin wadannan kasashe ke cika shekaru 6 da kafuwa.

Bitar ayyukan da kungiyar UFL mai cibiya a birnin Alge ta gudanar daga shekarar 2010 har zuwa yanzu, a kasahen da suka hada da Mauritania da Burkina Faso da Chadi da Algeria da Mali da Libiya da Nijar da kuma Najeriya wadda ta shiga sahu daga bisani na daga cikin abubuwan da wannan taro zai karkata a kansu.

Taron dai zi mayar da hankali kan hanyoyin da zasu bayar da damar daukan wasu kwararan matakan tunkarar matsalar ta’addancin da ke ci gaba da yaduwa, hakan yasa shugaban hukumar samar da bayanai na kasar Nijar Janal Lawal Shehu Kore, ya bukaci mahalartan wannan taro da su dage don bullo da dabarun karfafa ayyukan samar da bayanai na hakika wadanda za a musanya a tsakanin wannan yanki.

Shugaban kungiyar UFL mai baring ado Kanal Mohammad, ya bayyana cewa yankuna da yawa sunyi koyi da ayyukan wannan kungiya, wadda tayi fice wajen tattara bayanai da musayarsu a tsakanin kasashen membobinta. Saboda haka ya gargadi jami’an kungiyar samar da bayanan kungiyar da cewa kada halin karancin kayan aikin da ake fuskanta ya katse musu hanzari.

Kasar Nijar ta fuskanci munanan hare haren ta’addanci a shekarun baya bayan nan galibi daga kasashe makwabta irin su Mali da Najeriya, lamarin da wasu ‘yan kasar ke daura alhakin faruwarsa akan raunin matakan harhada bayanai.

Domin karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:39 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG