Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar al-Shabab ta kashe akalla mutane 30 a Somalia jiya Lahadi


Gawarwakin wasu cikin wadanda suka rasa rayukansu
Gawarwakin wasu cikin wadanda suka rasa rayukansu

Hukumomi a Somalia sun ce akalla mutane 30 aka kashe a jiya Lahadi bayan da wasu tagwayen bama-bamai suka tashi a garin Baidoa.

‘Yan sanda da hukumomin karamar hukumar garin sun ce lamarin ya faru ne a tsakiyar garin na Baidoa, wanda ke da tazarar tafiyar kilomita 245 daga Mogadishu babban birnin Somalia, kuma harin farko wanda aka dasa bam a wata mota ya auku ne yayin da ake hada-hadar kasuwanci.

Harin na biyu kuwa, wani dan kunar bakin wake ya tarwatsa kansa a wani gidan cin abinci.

Hukumomin sun ce baya ga mutane 30 da suka mutu, akalla wasu 40 kuma sun jikkata

Wadannan hare-hare na zuwa ne kwanaki biyu bayan da wasu munanan hare-hare da aka kai a kasar wadanda suka kashe mutane 25 kana wasu 65 suma suka jikkata a Mogadishu.

Kungiyar Al Shabab da ake alakantawa da ta Alqaeda ta dauki alhakin kai wadannan hare-hare.

Wani cikin wadanda suka jika a harin na Somalia
Wani cikin wadanda suka jika a harin na Somalia

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG