Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Isan Zazzau Umar Shehu Idris Ya Rasu


Dan Isan Zazzau, Alhaji Umar Shehu Idris (Hoto: Facebook/Masarautar Zazzau)
Dan Isan Zazzau, Alhaji Umar Shehu Idris (Hoto: Facebook/Masarautar Zazzau)

“Kafin rasuwarsa, Alhaji Umar Shehu Idris dai yana rike da mukamin Mataimakin Magatakardan Majalisar Masarautar Zazzau.” Sanarwar da masarautar ta fitar ta ce.

Msarautar Zazzau da ke jihar Kaduna a arewa maso yammaci ta sanar da rasuwar Dan Isan Zazzau, Alhaji Umar Shehu Idris.

Cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafukan sada zumunta, Masarautar ta ce a ranar Talata Allah ya yi wa Idris rasuwa.

“Cikin alhini da juyayi muke sanar da rasuwar Alhaji Umar Shehu Idris Dan Isan Zazzau wanda Allah Ya yi ma rasuwa da ranan yau.

“Kafin rasuwarsa Alhaji Umar Shehu Idris dai yana rike da mukamin Mataimakin Magatakardan Majalisar Masarautar Zazzau.” Sanarwar ta ce.

“Za a sanar da lokacin da za a gudanar da Jana'izar Marigayi San Isan Zazzau a nan gaba.

Da fatan Allah Ya jikanshi da rahamanSa, ameen.”

“Muna sanar da jama'a cewar za a gudanar da Jana'izar Marigayi Dan Isan Zazzau Alhaji Umar Shehu Idris ne a Kofar Fadan Mai Martaba Sarkin Zazzau a gobe (Laraba) da karfe 11:00 na Safiya.”

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG