Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Peter Obi Ya Kalubalanci Nasarar Tinubu A Kotu


Dan takarar LP, Peter Obi yayin taron manema labarai (Hoto: Facebook/Peter Obi)
Dan takarar LP, Peter Obi yayin taron manema labarai (Hoto: Facebook/Peter Obi)

A karar da ya shigar, Obi da jam’iyyarsa sun ce 'yan Najeriya ba Tinubu da Kashim Shettima suka zaba ba.

Dan takarar jam’iyyar Labor Party (LP) a Najeriya, Peter Obi, ya shigar da kara a kotun da ke sauraren kararrakin zabe a Abuja, inda ya kalubalanci nasarar dan takarar APC Bola Tinubu a ranar Talata.

A karar da ya shigar tare da jam’iyyarsa mai lamba CA/PEPC/03/2023, Obi ya nemi kotun da ta soke nasarar da dan takarar jam’iyyar APC, Bola Tinubu ya samu a zaben ranar 25 ga Watan Fabrairu.

Gidan talbijin na Channels ya ruwaito cewa Obi na neman a soke zaben ne saboda a cewar shi, ba Tinubu 'yan Najeriya suka zaba ba, saboda haka, hukumar zabe ta INEC ta karbe takardar shaidar lashe zabe da ta ba shi.

A karar da ya shigar, Obi da jam’iyyarsa na kalubalantar Tinubu, da zababben mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima.

Hukumar zabe ta INEC ta ayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa a watan da ya gabata, bayan da ya samu kuri’a sama da miliyan 8.7.

Ya doke dan takarar jam’iyyar adawa ta PDP Atiku Abubakar wanda ya samu kuri’a miliyan 6.9 sai Obi da ya zo na uku da ya samu kuri’a miliyan 6.1.

Sai dai jam’iyyar ta LP da Obi sun ce zaben ba sahihi ba ne saboda an yi arangizon kuri’u.

XS
SM
MD
LG