Kotun kolin kasar Senegal ta yanke cewa Abdoulaye Wade na iya tsayawa takarar neman wa’adin mulki na uku, hukuncin da ya sa jama'a bayyana rashin yarda cikin fushi.
Kamfanin dillancin Reuters ya ce, wani talbijin din Dakar ya ce dan sanda daya ya mutu sanadiyar raunukan da ya samu a kan shi a lokacin da su ke doke-doke da masu zanga-zanga.
Shaidu sun ce masu zanga-zangar na kona tayoyi, da kifar da motoci bayan da kotun kolin ta gabatar da hukuncin na ta da yammacin jiya Jumma’a.
Shugaban kasar mai ci dan shekaru 85 ya na cikin ‘yan takara, amma kotun ta yi watsi da takarar shararren mawakin kasar Youssou N’Dour.
Bayan hukuncin ‘yan sanda sun harba barkonon tsohuwa domin tarwatsa masu zanga-zangar da ke jifan su da duwatsu, da kuma kona tayoyi a tsakiyar birnin Dakar.
Kafin ma kotun ta yanke hukuncin daruruwan magoya bayan ‘yan hamayya sun yi jerin gwano a titunan birnin Dakar su na rera wakokin nuna rashin yardar su da shugaba Wade ya sake tsayawa takarar neman wa’adin mulki na uku.
Youssou N’Dour ya gayawa manema labarai cewa kundin tsarin mulkin kasar ya bayyana a fili karara cewa shugaba Wade ba shi da ‘yancin sake tsayawa takara.
Da safiyar nan ta yau Asabar masu zanga-zangar sun ce za su yi jerin gwano zuwa fadar shugaban kasar.