Shugabannin kungiyar Tarayyar Afrika sun fara wani taron wuni biyu yau lahadi a Addis Ababa tare da zaben sabon shugaban kungiyar ta hadin kan kasashen nahiyar Afrika.
An zabi shugaban kasar Benin Yayi Boni a matsayin sabon shugaban na wa’adin jagorancin shekara daya. Yayi Boni ya karbi shugabancin kungiyar ne daga hannun shugaban kasar Equatorial Guinea Teadoro Obiang Nguema.
Babban magatakardar Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon yana daya daga cikin wadanda suka fara gabatar da jawabai a taron da aka gudanar a sabuwar shalkwatar da kasar China ta gina da kudinta, kasar da ta kasance abokiyar cinikayyar kasashen nahiyar Afrika.
Mr. Ban ya shaidawa shugabannin kungiyar tarayyar Afrikan cewa tilas ne yi adalci a zabukan da za a gudanar a kasashe 25 na nahiyar bana, da suka hada da zaben shugabannin kasa da na ‘yan majalisa da kuma na shugabannin wakilai da shugabannin jihohi da kananan hukumomi a jiha.
Ya yi kira ga gwamnatin kasar Sudan da Sudan ta kudu su warware banbance banbancen dake tsakaninsu a kan albarkatun mai dake kan iyakar kasar.
Babban magatakardan MDD ya kuma bayyana cewa, kasar Samaliya da take fama da tashin tsashina tana iya samun kyakkyawar makoma.
2Ana kyautata zaton shugabannin kungiyar tarayyar Afrikan zasu tattauna a kan rikicin kasar Somaliya su kuma sake nazarin gardamar dake tsakanin Sudan da Sudan ta Kudu.