Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Putin Ya Ba Wa Ba’amurke Snowden Izinin Zama Dan Kasar Rasha


RUSIA-SNOWDEN
RUSIA-SNOWDEN

Hukumomin Amurka sun kwashe shekaru suna son a dawo da shi Amurka domin fuskantar shari’a kan laifukan leken asiri.

A ranar Litinin ne shugaba Vladimir Putin ya bai wa tsohon dan kwangilar a sashin leken asirin Amurka ,Edward Snowden, izinin zama dan kasar Rasha, shekaru tara bayan ya fallasa yawan ayyukan sa ido na sirri da hukumar tsaron kasa ta NSA.

Shugaban Rasha Vladimir Putin
Shugaban Rasha Vladimir Putin

Snowden, mai shekaru 39, ya tsere daga Amurka, yayin da aka kuma ba shi mafaka a Rasha, bayan da ya fallasa wasu bayanan sirri a shekarar 2013, wadanda suka bayyana dimbin ayyukan sa ido na cikin gida da na kasashen waje da hukumar ta NSA ta gudanar, inda ya yi aiki a da.

Tsohon Ma'ikacin leken asirin Amurka Edward Snowden
Tsohon Ma'ikacin leken asirin Amurka Edward Snowden

Snowden, wanda tsohon dan kwangila ne da Hukumar Tsaro ta Amurka, an ba shi izinin zama na dindindin a kasar Rasha a shekarar 2020, kuma a lokacin ya ce ya shirya neman zama dan kasar Rasha, ba tare da soke takardar zama dan kasar Amurka ba.

Snowden ya dauki kansa a matsayin mai fallasa bayanan sirri, kuma a lokacin da ya fallasa bayanan sirrin na Amurka, wasu masu sukar gwamnatin Amurka sun yabe shi a matsayin jarumin da ke gaya ma gwamnati gaskiya. Sai dai jami'an gwamnati da dama sun ce sun yi matukar kaduwa da bayanan da aka samu tare da yin kira da a gaggauta kama shi tare da gurfanar da shi gaban kuliya.

Nan take ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta shiriritar da sabon matsayin Snowden da ya samu a Rasha, tana mai cewa “da yuwuwar a shigar da shi aikin soja” don yaki ma Rasha a hare-haren da ta kai watanni bakwai a Ukraine.

Duk da rade-radin da ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta yi, lauyan Snowden Anatoly Kucherena ya ce Snowden ba zai shiga cikin tarin kusan sojoji dubu 300 da Putin ya zartar a makon da ya gabata domin taimaka wa Rashan yakin Ukraine, tun da Snowden bai taba shiga sojan Rasha ba.

Hukumomin Amurka sun kwashe shekaru suna son a dawo da shi Amurka domin fuskantar shari’a kan laifukan leken asiri.

Sunan Snowden ya bayyana ba tare da fadar Kremlin ba a cikin dokar da Putin ya bayar ta ba da izinin zama dan kasa kan wasu mutane 72 da aka haifa a kasashen waje.

Daga baya Snowden ya fitar da wani sakon Twitter, yana mai cewa “Bayan rabuwa da iyayenmu na tsawon shekaru, ni da matata ba ma son a raba mu da ’YA’YANMU,”

XS
SM
MD
LG