Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Tsaida Ranakun 19 Da 20 Ga Watan Maris Domin Ci Gaba Da Sauraron Shari'ar Nnamdi Kanu


Nnamdi Kanu, a tsakiyar wasu lauyoyi a kotu
Nnamdi Kanu, a tsakiyar wasu lauyoyi a kotu

Babbar Kotun Tarayya dake Abuja ta tsayar da ranakun 19 da 20 ga watan Maris mai kamawa domin ci gaba da sauraron shari'ar jagoran haramtacciyar kungiyar 'yan awaren Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu dake fuskantar tuhuma akan zargin cin amanar kasa.

Alkalin kotun, Mai Shari'a Binta Murtala Nyako ta tsaida ranakun ne bayan sauraron bayanan lauyan mr. Kanu, Alloy Ejimakor wanda ya bukaci kotun ta bada belin wanda yake karewa a bisa dalilai na rashin lafiya.

Saidai lauyan gwamnatin tarayya kuma wanda ya shiga shari'ar a matsayin shugaban tawagar lauyoyinta, mr. adegboyega awomlowo ya kalubalanci bukatar bada belin, inda yace Hukumar Tsaron Farin Kaya ta DSS na da dukkan abinda ake bukata domin duba lafiyar Mr. Kanu.

Gwamnatin tarayya ta shigar da sabbin tuhume-tuhume 15 dake da nasaba da ta’addanci da cin amanar kasa akan Mr. Kanu a shekarar 2021.

An gurfanar da shi a gaban kotu a watan Yulin 2021 bayan da aka taso keyarsa daga kasar Kenya.

Alkalin Kotun, Mai Shari’a Binta Murtala-Nyaku ta soke 8 daga cikin tuhume-tuhumen 15 bayan data yanke hukunci akan korafe-korafen da lauyan Mr. Kanu ya shigar tunda fari yana kalubalantar sahihancin tuhume-tuhumen.

Mr. Kanu dai na kalubalantar hukuncin kotun na ci gaba da sauraron 7 daga cikin tuhume-tuhume 15 kasancewar korafin daya shigar tunda fari ya bukaci a yi watsi da gaba dayan tuhume-tuhumen.

Kotun Daukaka Kara tayi watsi da gabadayan tuhume-tuhume akan Mr. Kanu dogaro da cewar gwamnatin tarayya tayi kuskure a hanyoyin da ta bi wajen taso keyarsa zuwa Najeriya.

Saidai Kotun Koli ta rushe hukuncin na Kotun Daukaka Kara.

Kotun Kolin tayi togaciya da cewar matakin da gwamnatin tarayyar tayi amfani dasu wajen kama Mr. Kanu basu isa su rushe gabadayan shari’ar ba.

An umarci wanda ake kara daya koma gaban Babbar Kotun Tarayya domin ci gaba da fuskantar shari’a a daidai inda aka tsaya tunda fari.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG