A yau Laraba, wata babbar kotun jihar Kano ta bada umarnin mikawa shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dr. Abdullahi Ganduje, da sauran wadanda ake tuhuma tare da shi a shari’ar cin hanci da rashawa da suke fuskanta sammaci ta wasu hanyoyin na daban.
Gwamnatin Kano na tuhumar Ganduje da mai dakinsa, Hafsat Umar da wadansu mukarrabansa da zargin aikata laifuffuka 10 masu nasaba da cin hanci da almundahana da karkatar da kudaden al’umma na biliyoyin Naira.
A yayin zaman kotun, lauyan wadanda ake kara, Nureini Jimoh, ya kalubalanci bayyanar da babban lauyan bangaren masu kara, Yau Adamu, yayi gaban kotun, inda yace an riga an baiwa wani mutum guda izinin tsayawa bangaren a shari’ar.
Ya'u Adamu ya maida martani ta hanyar shaidawa kotun cewar saboda wannan kalubale, Barista Zahraddeen Kofar Mata ya gabatar da bukatar saurare da yanke hukunci bisa la’akari da uzurin bangare daya na gajeran wa’adi.
Mai Shari’a Amina Adamu-Aliyu ta rushe kalubalantar da Jimoh tare da amincewa da umarnin, biyo bayan bukatar da Kofar-Mata, wanda ke wakiltar bangaren masu gabatar da kara ya gabatar.
Haka kuma, Mai Shari’a Amina Adamu Aliyu ta umarci bangarorin 2 dake cikin shari’ar dasu gabatarwa kotu izinin bayyana a gaban kotun da suke da shi.
Ta kuma dage zaman kotun zuwa ranar 11 ga watan Yuli mai kamawa domin cigaba da sauraron karar.
Dandalin Mu Tattauna