Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

EFCC Ta Ba Da Belin Akanta Janar Na Najeriya


Shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa - a dama (Instagram/EFCC)
Shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa - a dama (Instagram/EFCC)

Ana zargin Idris da karkatar da sama da naira biliyan 80, lamarin da ya sa hukumar ta EFCC ta tsare shi a tsakiyar watan Mayun da ya gabata.

Hukumar da ke yaki da masu yi wa arzikin kasa zagon kasa ta EFCC a Najeriya ta ba da belin Akanta-Janar na gwamnatin tarayyar kasar Ahmed Idris.

Ana zargin Idris da karkatar da sama da naira biliyan 80, lamarin da ya sa hukumar ta EFCC ta tsare shi a tsakiyar watan Mayun da ya gabata.

Gidan talabijin na Channels ya ruwaito kakakin EFCC Wilson Uwajeren yana tabbatar da sakin Idris, wanda aka dakatar daga aiki bayan da EFCC ta kama shi.

Bayan da ta kama shi a Abuja, babban tarayyar Najeriya, EFCC ta ce ta yi ta gayyatar Idris zuwa ofishinta amma yana kin zuwa, lamarin da ya kai ga ta damke shi.

‘Yan makonnin bayan kama Idris, hukumar ta EFCC ta kama tsohon gwamnan jihar Imo Sanata Rochas Okorocha bisa wani umarni da kotun tarayya ta bayar.

Ana zarginsa ne da karkatar da kudade sama da biliyan 2 a lokacin yana gwamnan jihar ta Imo wacce ke kudu maso gabashin Najeriya.

A farkon makon nan kotu ta ba da belin Okorocha a kan kudi naira miliyan 500.

XS
SM
MD
LG