Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Dage Shari'ar Nnamdi Kanu Har Sai Illa Masha Allahu


Nnamdi Kanu, a tsakiyar wasu lauyoyi a kotu
Nnamdi Kanu, a tsakiyar wasu lauyoyi a kotu

A watan Yunin 2021 aka dawo  da Kanu zuwa Najeriya kuma tun lokacin yake tsare tare da fuskantar shari'a a kan zargin ta'addanci.

A yau Litinin shugaban haramtacciyar kungiyar masu rajin kafa kasar Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu ya kalubalanci hurumin kotu a kan zargin ta'addancin da ake masa lokacin da ya bayyana gaban Mai Shari'a Binta Nyako ta babbar kotun tarayya domin ci gaba da sauraron shari'arsa.

Duk da dagewar da Kanu ya yi a kan cewa Mai Shari'a Nyako ba ta da hurumin sauraron karar, alkaliyar ta dage sauraron har illa masha Allahu.

A watan Yunin 2021 aka dawo da Kanu zuwa Najeriya kuma tun lokacin yake tsare tare da fuskantar shari'a a kan zargin ta'addanci.

Shari'ar ta samu tsaiko bayan da Mai Sharia Nyako ta tsame kanta daga sauraron karar bayan da wanda ake tuhuma ya gabatar da bukatar yin hakan da baki a ranar 24 ga watan Satumban 2024.

Kai tsaye shugaban kungiyar ta IPOB ya shaidawa alkaliyar cewa ya yanke kauna akan yadda take gudanar da shari'ar.

Dandalin Mu Tattauna

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 3:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:02:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG