Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun Koli Ta Amince a Fara Aiwatar Da Wani Sashen Dokar Hana Shiga Amurka


Kotun kolin Amurka dake Washington, April 4, 2017.
Kotun kolin Amurka dake Washington, April 4, 2017.

A karon farko kotun kolin Amurka ta ce, za a iya fara aiwatar da wani sashe na umurnin da shugaba Donald Trump ya bayar kan hana wasu 'yan kasashe mafiya rinjayen Musulmi shiga Amurkan na dan wani tsawon lokaci, ko da yake kotun ta ce akwai mutanen da wannan lamari ba zai shafa ba.

Kotun kolin Amurka ta ce za ta yi dubi kan karar da shugaba Donald Trump ya shigar game da umurnin da ya bayar na neman a tsawwala dokokin shiga Amurkan, inda ta yanke hukuncin cewa wani sashen dokar zai iya fara aiki.

Umurnin na shugaba Trump ya hana kasashe shida wadanda ke da mafi rinjayen musulmi shiga Amurka na tsawon kwanaki 90. Kana za a hana ‘yan gudun hijra daga kasashen shiga Amurkan na tsawon kwanaki 120.

A baya wasu kotuna biyu daban-daban dakejihohin Hawaii da Maryland sun dakile shirin aiwatar da dokar, inda suka yake hukuncin daban-daban.

Sai dai kotun kolin ta dauki wata makoma daban, inda ta ba da kofar a fara aiwatar da dokar akan kasashen Libya da Iran da Somalia da Sudan da Syria da kuma Yemen tare da jingine shirin karbar ‘yan gudun hijrar.

Sai dai alkalan kotun sun ce dokar ba za ta yi aiki akan ‘yan kasashen ba, wadanda suke alaka ta gaske da wani mutum ko kuma wani kamfani ko kungiya a nan Amurka.

Misali, dokar ba za ta yi aiki akan wadanda suke da alaka ta jini da wani a nan Amurka ba, ko dalibi ko masu neman gurbin karatu a kwaleji ko jami’a ko kuma ma’aikata ko wani da aka baiwa aiki a Amurka ba.

A baya Shugaba Trump dai ya ce wannan doka za ta fara aiki nan da sa’oi 72 yayin da ya bayyana a wata sanarwa cewa wannan hukuncin da kotu ta yanke “wannan babbar nasara” da suka samu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG