Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Republican Sun Fidda Daftarin Dokar Kiwon Lafiya.


Shugaban masu rinjaye a majalisar datiijan Amurka Mitch McConnell.
Shugaban masu rinjaye a majalisar datiijan Amurka Mitch McConnell.

Bayan an shafe makonni wakilan majalisar dattijan suna gudanar da shawarwari cikin sirri.

Bayan shafe makonni suna tattaunawa a kadaice, yan jam’iyar Reuplican a majalisar dattijai sun fitar da daftarin kudurin yiwa tsarin kiwon lafiyar Amurka garambawul, da nufin sokewa da kuma maye gurbin tsarin kiwon lafiya na gwamnatin da ta gabata da ake kira “Obamacare”, abinda ya janyo kushewa daga ‘yan jam’iyar Democrat yayinda wadansu ‘yan jam’iyar Republicans masu sassaucin ra’ayi da kuma masu ra’ayin rikau a jam’iyar tasu suke bayyana damuwa.

A wani abinda tamkar cika alkawarin da jam’iyar Republican ta dade tana yiwa masu kada kuri’a cewa zasu kawo karshen dokar da ta tilastawa dukan Amurkawa sayen inshorar kula da lafiyarsu, da janye tallafin da gwamnatin tarayya ke badawa na sayen inshorar, da kuma zaftare kudin da ake kashewa wajen jinyar gajiyayyu.

Shugaban masu rinjaye na majalisar dattijai Mitch MacConnel yana kokarin gain majalisa ta kada kuri’a a kai mako mai zuwa, kafin majalisar ta tafi hutun hudu ga watan Yuli, ‘yan jam’iyar Democrats sunki amincewa da gaggauta kada kuri’a a kan tsarin inshoran da aka shata a asirce ba tare da bada dama a yi bayanai gabam kwamiti ba.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG