Sojojin Iszaela sun kakkabo wani jirgin Syria mara matuki na liken asiri a yau asabar a kusa da bakin iyaka, kamar yadda sojojin kasar ta Israela ke cewa.
Sojojin dai sun harbo wannan jirgin ne bayan da suka cilla wani jirgi mai saukar ungulu, bayan da jirgin mara matuki ya tsallaka yankin Golan da ya dunfari cikin Izraela.
Ministan tsaron kasar ta Izraela Avigor Lieberman ya fada acikin wata sanarwa cewa ba gudu ba ja da baya duk wanda yayi kokarin gwada karfin su tare da kin mutunta diyaucin mu,na kasa mai cikakken ‘yancin cin gashin kanta to zai hadu da hushin mu.
Shi dai yankin na Golan shine ya raba tsakanin Iszaela da Syria tun lokacin da aka cimma matsayar dakatar da bude wa juna wuta a ckin shekarar 1973, sai dai wannan wurin yana fuskanttar samar da burbushi-burbushin yakin basasan kasar ta Syria tun daga shekarar 2011.
A cikin watan satunba sojojin Syria sunce jirgin yakin kasar Izraela ya bankadi daya daga ciki sansanin sa inda har ya kashe mutane biyu.
Facebook Forum