An kama tsohon jami'in rundunar sojan ruwa na Indiya, Kulbhushan Jadhav, tun watan Maris din shekarar 2016 a Kudu maso Yammacin yankin Bluchistan na kasar Pakistan.
Daga baya wata kotun soja ta saurari shari’a ta kuma yanke masa hukuncin kisa, ta yanke hukuncin cewa an sami kwamandan rundunar sojan ruwan Indiya da laifin leken asiri da kuma ta’addanci akan kasar Pakistan.
A jiya Juma’a ne ma’aikatar harkokin waje ta bukaci a shirya Jadhav ya gana da matarsa, tana mai cewa a hukumance an samar da ofishin diplomasiyyar Indiya dake Islamabad akan wannan shawara da aka yanke.
Kasar Indiya dai ta yarda da cewa Jadhav tsohon ma’aikacin rundunar sojan ruwan kasar ne, amma ta yi watsi da tuhumar da aka yi masa, tana mai cewa bata da tushe, domin Jadhav bashi da wata alaka da gwamnati.
Indiya dai tayi zargin cewa anyi garkuwa da Jadhav ne a Iran, aka kuma ‘dauke shi zuwa Baluchistan.
Facebook Forum