A wata sanarwa a jiya Alhamis Saud al-Mojeb yace an sake mutane bakwai a cikin wadanda aka tsaren ba tare da wani caji ba, amma ana ci gaba da tsare saura 201. Gwamnati ta kuma dora hannu a kan takardun banki 1,700.
Sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson, yace ya tattauna da ministan harkokin wajen Saudi Arabia, Adel al-Jubeir a ranar Talata. Sakataren yace ya fahimci cewa ya zuwa yanzu ana tsare dasu ne amma ba an kamasu bane kuma ana tattara shaida na laifin da ake ganin sun aikata da zummar gyara al’amura.
Masu sukar gwamnatin Saudia sun ce ana gudanar da wannan bincike ne don kawar da wasu jami’an gwamnatin Saudian da kuma maida abokan gaba saniyar ware yayin da yarima Mohammad bin Salman yake jagorantar sabuwar hukamar yaki da rashawa.
Sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson ya fada a yau Juma'a cewar babu wata alamar dake nuna Saudia ta tsare firayim ministan Lebanon Sa’ad al-Hariri bada son ransa ba.
Hariri ya bada sanarwar cewar zai yi murabus a matsayin Firayi ministan Lebanon yayin da yake Saudi Arabia a ranar Asabar da ta gabata.
Facebook Forum