Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Koriya ta Arewa Ta Kama Ba'Amurke


Shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong Un tare da sojojinsa.
Shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong Un tare da sojojinsa.

Koriya Ta Arewa ta ce ta damke wani ba-Amurke dan yawon bude ido ran 10 ga watan nan na Afrilu saboda ya yi matukar sabawa ma dokokinta.

Kafar yada labaran gwamnatin Koriya Ta Arewar ta ruwaito cewa Miller Matthew Todd dan shekaru 24 da haihuwa ya yaga takardar visa dinsa yayin da ya ke shiga kasar ta Koriya Ta Kudu da cewa shi mafaka ya ke nema a kasar.

Kafar yada labaran ta ce jami'ai na binciken wannan halin rashin natuwa na wannan dan yawon bude idon.

An sami wannan rahoton ne yayin da Shugaban Amurka Barack Obama ke ziyartar Koriya Ta Kudu don tattaunwa da Shugaba Park Geun-Hye.

Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ce ta na sane da wannan rahoton kuma ta shiga tuntubar Sweden, wadda ke wakilta Amurka kan harkokin da su ka shafi Amurkar a Koriya Ta Arewa.
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG