Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Da Koriya Ta Kudu Sun Kara Shirin Ko-Ta-Kwana


Sojojin Koriya ta Kudu su na kallon Arewa da tabaron hangen nesa a kusa da kauyen Panmunjom dake bakin iyakarsu April 10, 2013.
Sojojin Koriya ta Kudu su na kallon Arewa da tabaron hangen nesa a kusa da kauyen Panmunjom dake bakin iyakarsu April 10, 2013.

Gwajin makami mai linzamin da ake tsammanin Koriya ta Arewa zata yi, ya sanya makwabtanta sun kara zaman shirin ko-ta-kwana na sojojinsu.

Amurka da Koriya ta Kudu sun kara daura shirin ko-ta-kwana a saboda gwajin makami mai linzamin da ake kyautata zaton Koriya ta Arewa zata yi.

Kamfanin dillancin labaran Yonhap na Koriya ta Kudu ya fada a yau laraba cewa rundunar sojojin hadin guiwa ta kasashen biyu ta kara matsayin zaman shirin ko-ta-kwananta zuwa matakin da ake kira "WatchCon 2," matsayin dake nuna alamun akwai "mummunar barazana."

An ce Koriya ta Arewa tana shirye-shiryen karshe na gwajin makami mai linzami dake cin matsakaicin zango, abinda ya sa makwabtanta suke barci ido daya a bude.

Wasu masu fashin baki su na kyautata zaton za a gudanar da wannan gwaji a daidai lokacin da za a gudanar da bukukuwan tuna ranar haihuwar mutumin da ya kafa kasar Koriya ta Arewa, Kim Il Sung, a ranar litinin mai zuwa.

Ministan harkokin wajen Koriya ta Kudu, Yun Byung-Se, ya fadawa 'yan majalisar dokoki yau laraba cewa akwai yiwuwar Koriya ta Arewa zata yi gwajin daya daga cikin sabbin makamanta masu linzami a kowane lokaci daga yanzu.

Wannan sabon makami mai linzami mai suna Musudan, wanda ba a taba gwajinsa ba, yana iya kaiwa cikin Koriya ta Kudu ko Japan ko tsibirin Guam dake karkashin mulkin Amurka. Wasu rahotannin da ba a tabbatar da su ba sun ce Koriya ta Arewa tana shirin gwaje-gwajen wasu makaman masu linzami, duk a lokaci guda.
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG