Nan da nan Koriya ta Kudu ta mai da martani a yau dinnan Litini, ta wajen barin wuta kan ruwayen Koriya ta Arewa. Jami'ai sun ce babu wani harbin da ya fada bisa rairayin kasa daga dukkan bangarorin, a tsawon kan iyakar da ke yamma, kuma babu wanda ya ji rauni. Koriya ta Kudu ta ce an samar da mafaka ga wasu mazauna tsibiran da ke daura da kan iyaka don kauce ma tsautsayi.
Janar din sojan Amurka Paul Kennedy, ya ce atisayen na hadin gwiwa da ke gudana daga tazarar kilomita 360 daga birnin Seoul, bai da wata manufa ta siyasa.
A 'yan makwannin nan, Koriya ta Arewa ta yawaita barazanar baka, ta kuma harba jerin rokoki da makamai masu linzami cikin ruwaye, nisa da gabobin yankin ruwayen na na koriya.
Koriya ta Arewa ta yi barazana jiya Lahadi, ta gudanar da, abin da ta kira, "wani sabon nau'in gwajin makamin nukiliya" bayan da Kwamitin Sulhun MDD ya yi Allah wadai da kaddamar da makamai masu linzamin da Koriya ta Arewa ta yi kwanan nan.
Malcolm Cook, wani manazarci a wata cibiyar nazarin harkokin Kudancin Asia da ke Singapore, ya gaya ma Muryar Amurka cewa wannan al'amarin na nuna cewa a yanzu Koriya ta Arewa ta iya kirkiro bama-baman nukiliya.
Wani jawabin da ya fito daga Ma'aikatar Harkokin Wajen Koriya ta Arewa a yau dinnan Litini ya ce ba zai yiwu Kwamitin Sulhun ya rufe ido Amurka na ta atisayen yakin makamin nukiliya sannan kuma ya caccaki sojojin Koriya Ta Arewa don kawai su na atisayen kare kai ta kaddamar da harbin rokoki ba.
Bayan da Koriya ta Arewa ta harba makamai masu linzami na matsakaicin zango cikin ruwa nesa da gabar gabas ta ruwayen na Koriya ranar Laraba, sai Kwamitin Sulhun na MDD ya yi Allah wadai da hakan da wayewar gari, da cewa hakan ya saba ma kudurin MDD.
Koriya ta Arewa kan bayyana atisayen soja da akan yi tsakanin Koriya ta kudu da Amurka a matsayin atisayen mamaya.