Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Koriya Ta Arewa Ta Ce Zata Abkawa Koriya Ta Kudu


Sojojin Koriya ta Arewa suna atisaye. Maris 20, 2013. REUTERS/KCNA (NORTH KOREA - Tags: POLITICS MILITARY) ATTENTI
Sojojin Koriya ta Arewa suna atisaye. Maris 20, 2013. REUTERS/KCNA (NORTH KOREA - Tags: POLITICS MILITARY) ATTENTI

Koriya ta Arewa ta sake fitowa da wata sabuwar barazanar cewa zata abkawa makwapciyarta Koriya ta Kudu da hari saboda ta huce haushinta kan zanga-zangar da mutanen Koriya ta Kudu suka yi, abinda Koriya ta Arewa tace ya nuna kamar sun rena ta.

WASHINGTON, D.C - Rundunar sojan Koriya ta Arewa ta barazanar cewa zata dauki matakan da bata fayyace ba idan hukumomin Koriya ta Kudu basu nemi gafara ba akan zanga-zangar da mutanensu suka yi jiya Litinin, inda har suka kona wasu gumakan shugabannin Koriya ta Arewa din.

Sanarwar da hukumomin na Koriya ta Arewa suka bada a cuikin kafofinsu na watsa labarai sun yi anfani da irin lafuzzan da suka saba masu zafi, kamar cewa zasu yi anfani da “hammer mai kaifi” wajen yin ramuwar gayya akan abinda suka kira “wannan mummunan hali abin kyama” da masu zanga-zangar suka nuna.

A nan Washington, shugaba Barack Obama yace yana sa ran za’a ci gaba da ganin irin wannan hali na tsokana da neman tada-zaune tsaye a wajen shugabannin na Koriya ta Arewa.
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG