Kamfanin Dillancin Labaran Gwamnatin Koriya Ta Arewa ya fadi yau Asabar cewa kasar, “ba za ta taba amfani da makaman nukiliya ko kuma ta kai makaman nukiliya zuwa wata kasa, ko kuma ta baiwa wasu fasahar kirkiro nukiliya ba, ko da bisa wani sharadi ne, idan ba dai akwai wata barazana ta nukiliya ko kuma an auna Koriya Ta Arewa da makamin nukiliya ba.
Sojojin Koriya Ta Arewa su na kuma shirin daina amfani da makamai masu linzami masu dogon zango, kuma sun ce daga yau din Asabar za su dakatar.
Koriya Ta Arewa ta ce gwamnati na kokarin canja alkiblarta a matsayin kasa ta kuma mai da hankali kan inganta tattalin arziki.
Wannan na faruwa ne kasa da mako guda da Shugaban Koriya Ta Arewa zai gana da Shugaban Koriya Ta Kudu Moon Jae-in a bayan fagen wani babban taro a kokarinsu na kawo karshen takaddama kan batun na nukiliya da ake yi a yankin ruwan Koriya. Amurka da Koriya Ta Arewa na shirin yin wani taro na dabam, kodayake har yanzu ba a sa rana.
Facebook Forum