Amma jami'an Amurka sun ce Washington da kawayenta suna ci gaba da sa ido sosai.
Babban mai Magana da yawun cibiyar tsaron Amurka Dana white ta shaidawa manema labarai a jiya alhamis cewa, tilas ne shugaban Syria Bashar al-Assad ya san cewa, duniya ba zata amince da amfani da makamai masu guba a kowanne irin hali ba.
A wata hira da kafar watsa labarai ta gwamnati RIA Novosti a yau jumma'a, Ministan harkokin kasashen wajen Rasha Sergei Lavrov ya ce Rasha ta yiwa Amurka da abokan kawancenta iyaka da abin da ba zata iya kauda kai ba tare da maida martani ba, kafin su kai harin sararin saman.
Harin da Amurka ta kai maida martani ne, kan harin da ake kyautata zaton na makaman nukiliya ne, da ya kashe fararen hula 40 a Douma a ranar 7 ga watan Afirilu. Kasar Amurka dai ta zargi Syria. Amma abokan kawancen Syria Damascus da Rasha sun musanta cewa ba ayi amfani da wadanan makaman ba.
Facebook Forum