Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rasha Ta Bukaci Amurka Ta Biyata Diyya Sakamakon Karin Haraji Akan Tama da Karafa


Shugaban Rasha Vladimir Putin
Shugaban Rasha Vladimir Putin

Biyo bayan karin haraji akan tama da karafa dake shigowa Amurka daga waje da gwamnatin Trump ta yi, kasar Rasha ta nemi diyya abun da kuma Amurka tayi watsi dashi tana cewa dokar kasa da kasa ta amince ya yi karin sabili da tsaro.

A jiya Alhamis ne Rasha ta bukaci Amurka ta biya ta diyya, sakamakon karin kudi harajin ta akan tama da karafa na kasar waje, wanda wannan Rashan ce ta ukku cikin jerin kasashen da ke da tasiri a kungiyar cinikayya ta duniya data bukaci hakan.

Ita ma China da kungiya tarayyar Turai har ma da India duk sunki amincewa da wannan karin suna cewa harajin an samar dashi ne kawai da zummar kare abubuwan da ake samar wa a cikin Amurka, wanda kuma ke bukatar diyya daga manyan kasashen da suke fitar da kayayyakin su.

Sai dai gwamnatin Trump bata yarda da wannan hanzarin da wadannan kasashen suka kawo ba game da neman diyya. Gwamnatin Amurka tace harajin na inganta harkokin tsaro ne kuma dokar kasa-da-kasa ta amince da hakan.

Sai dai kawai Amurka ta amince ta tattauna da kasar China, haka kuma ta shaidawa kungiyar tarayyar Turai da India cewa a shirye take ta tattauna dasu akan wasu batutuwa na daban amma batun neman diyya kam sam bata ma taso ba.

Sai dai wasu kawayen Amurka kamar su Australia, Canada, Kungiyar Tarayyar Turai,Korea ta Kudu duka an dage musu wannan karin harajin har sai an cimma matsaya da Amurkan.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG