Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Gudun Hijirar Rohingya Suna Fuskantar Bala'iN Ruwan Sama.


Matakan hana hana abaliyar ruwa barna a sansanin 'yan gudun hijira na kabilar Rohingya dake Bangladesh.
Matakan hana hana abaliyar ruwa barna a sansanin 'yan gudun hijira na kabilar Rohingya dake Bangladesh.

Jami'an hukumar kula da 'yan ci rani ta kasa da kasa ta koka kan karancin kudi da zata iya amfani dasu wajen inganta karfin matsugunin 'yan gudun hijirar.

Hukumar kula da bakin haure da 'yan-ci-rani ta kasa da kasa, tace bata da kudi da zata yi amfani da su domin kare 'yan kabilar Rohyingya da suke gudun hijira a wani sansani a yankin da ake kira Cox Bazar a Bangledash, daga ruwan sama mai tsananin gaske da ake hasashe zai fatatttaki yankin, wannan rahoton ma Lisa Schlein ce ta aiko dashi daga Geneva.

Ahalin yanzu dai ana ruwan sama a yankin amma ba mai tsanai ba. Amma masana yanayi suna hasashen ruwan saman zai karu kamar da bakin kwariya, da zasu hadasa ambaliya da gocewar laka, kuma zasu yi barna ainun ga bukkoki ko 'yan gine gine da 'yan gudun hijira ta Rohingya su fiyeda dubu 700 suke zaune, bayan da suka tsere daga makwabciyar kasa Myanmar.

Hukumomin agaji suna aiki ba dare ba rana, domin karfafa matsugunin 'yan gudun hijirar da yake cike makil da Bil'Adama, domin hana su rushewa sakamakon ruwan saman da ake tsammanin yana tafe.

Kakakin hukumar yace, kungiyar bata da kudin, domin kashi 7 cikin dari na kudi dala milyan 180 da hukumar take bukata.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG