Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ko Me Ake Ciki Game Da Batun Siriya?


Sakataren Harkokin Wajen Amurka John Kerry da Takwaransa na Rasha Sergei Lavrov a lokacin da suka ganawa dangane da rigingimun Syria.
Sakataren Harkokin Wajen Amurka John Kerry da Takwaransa na Rasha Sergei Lavrov a lokacin da suka ganawa dangane da rigingimun Syria.

Sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry, da takwaran aikinsa na Rasha, Sergei Lavrov, su na wani sabon yunkurin gudanar da taron neman zaman lafiya da aka jima ana jinkirtawa da nufin kawo karshen yakin basasar kasar Sham, ko Siriya.

A yau jumma’a birnin Geneva, jami’an biyu sun gana da wakilin MDD kan rikicin kasar Sham, Lakhdar Brahimi. Su na tattauna wani shirin kasar Rasha, kan yadda za a sanya makamai masu guba na kasar Sham karkashin kulawar kasa da kasa.

Kerry da Lavrov sun yarda zasu sake ganawa karshen watan nan a New York domin tattaunawa kan shawarwarin neman zaman lafiyar da rabon da a gudanar da su tun watan Yunin bara. Amma Kerry yace duk wani ci gaban da za a samu zai dogara ne a kan nasarar kawar da makamai masu guba na kasar Sham.

Kasar Sham ta shiga cikin wata yarjejeniyar haramta makamai masu guba a duniya, amma ta ce tana da wata gtuda kafin ta bayyana irin makamai masu guba da ta mallaka. Shugaba Bashar al-Assad ya fada jiya alhamis cewa zai rattaba hannu kan yarjejeniyar kawar da makamai masu gubar ne kawai idan har Amurka ta daina barazanar cewa zata kai masa farmaki.

A yau jumma’a, shugaba Vladimir Putin na kasar Rasha, ya yaba da shawarar kasar Sham ta shiga cikin yarjejeniyar da ta haramta amfani da makamai masu guba a duniya, yana mai fadin cewa wannan ta nuna kyakkyawar aniyar gwamnatin shugaba Bashar al-Assad, ta warware wannan rikicin.
XS
SM
MD
LG