Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jinkirta Kai Hari Kan Syria


Shugaban Amurka Barack Obama
Shugaban Amurka Barack Obama

Shugaban Amurka Barack Obama na nemar amincewar Majalisar Tarayyar Amurka don kai hari Syria

Shugaban Amurka Barack Obama ya jinkirta wani harin soji da ake kyautata zaton za a kai kan Syria, a maimakon hakan ya shaida ma Amurkawa cewa zai nemi amincewar ‘yan Majalisa don ya hukunta gwamnatin Syria saboda amfani da makaman gubar da ta yi.

A wani jawabin da ya yi jiya Asabar a Fadar White House, Mr. Obama ya ce ya yanke shawarar cewa ya kamata Amurka ta dau matakin soji a kan kadarorin gwamnatin Syria. To amma ya ce kodayake ya yi imanin cewa ya na da ikon ba da umurnin kai hari, ya na kuma ganin yana da muhimmanci kasar ta tattauna kan batun.

Daga bisani a jiya Asabar din, Shugaba Obama ya bukaci ‘yan Majalisun kasar su amince masa ya dau matakin soji kan Syria don a tauna tsakuwa a birkitar a kawar a kuma rage duk wata yiwuwar sake kai harin makaman guba nan gaba.

Amma Shugaba Obama ya ce babu wani abin da zai sa a yi amfani da sojojin kasa a Syria.

Ya bayyana abin da ya faru a Dimashku kusan makonni biyu da su ka gabata da cewa shi ne harin makaman guba mafi muni a karni na 21, sannan ya ce bai kamata Amurka ta yi kamar ba ta gani ba.

Shugabannin Majalisun Dokokin Murkan kuma sun mai da martani da cewa su na sa ran za a yi muhawara kan batun a Majalisun Dattawa da ta Wakilai bayan sun dawo daga hutu ran 9 ga watan Satumba.
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG