Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Obama Ya Ce Yaki Kawai Ba Zai Daidaita Siriya Ba


Shugaban Amurka Barack Obama
Shugaban Amurka Barack Obama

Shugaban Amurka Barack Obama ya ce yaki kawai ba zai magance matsalar Siriya ba. Sai an hada da hanyar siyasa.

Shugaban Amurka Barack Obama ya ce ba za a iya kawo karshen yakin basasar da ake gwabzawa a kasar Siriya ta hanyar soji kawai ba.

Da ya ke magana bayan ganawarsa da Shugaban kasar Faransa Francois Hollande jiya Jumma’a, a taron kasashe 20 masu karfin tattalin arziki (ko G20) a St. Petersburg na kasar Rasha, Mr Obama ya ce za a kai duk wani hari a Siriya ne, da zummar nakkasa karfin makaman gubar gwamnatin Siriya. To amma, ya ce, dole ne duniya ta cigaba da kokarin bullo da tsarin siyasar da zai kawo kwanciyar hankali, da cigaba, da zaman lafiya da kuma halacci a Siriya.

Shugaban kasar Faransa dai na goyon bayan kiraye-kirayen Mr. Obama na akai harin hadin gwiwa kan gwamnatin Assad da ke Dimashku, a matsayin martanin mummunan harin makaman gubar da aka kai kan fararen hula, a wasu wuraren da ke kusa da babban birnin kasar.

Shugaban Rasha Vladimir Putin, ya cigaba da nuna matukar adawa da yinkurin yammacin duniya na daukar matakin soji a Syria, kuma tare da goyon bayan China, Rasha ta hana Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya daukar mataki a wannan yakin basasar.

Jakadiyar Amurka a MDD Samantha Power, ta ce irin madaidaicin matakin soji da Amurka ke shirin daukawa a Siriya, shi ne mafi kankantan abin da ya kamata manyan kasashen duniya su yi.

Da ta ke magana a birnin Washington jiya Jumma’a, Samantha ta ce Shugaba Bashar al-Assad, ya jibge dinbin makaman guba, kuma abubuwan da su ka auku kwanan nan, wani dan kankanin abu ne daga cikin illar taren makamansa
XS
SM
MD
LG