Na farko yace, Rasha tana da dadadden tarihin hulda da kasar Rasha tun zamanin tsohon shugaban kasar, mahaifin Bashar, watau Hafiz Al-Assad. Na biyu bisa ga cewar Frofesa Boube Namaiwa, Rasha tana gani kamar akwai munafunci a ciki. Tana ganin kamar ana bada karfi ne kan abinda gwamnatin Syria ke yi ba tare da kula da abinda ‘yan tawayen ke aikatawa ba.
Dalili na uku inji Farfesa Namaiwa shine, Rasha da China suna yunkurowa, suna so su taka rawa can dabam ba irin wadda kasashen turai suke takawa ba. Watau sun zama kamar kishiya ne da Amurka. Saboda haka duk abinda Amurka zata yi zasu ce ba daidai bane.
Na hudu kuma shine, suna shakkun abinda zai biyo bayan kaiwa Syria hari, sabili da sun ga an yi a Iraq, an yi a Libya, an yi a Afghanistan, an yi a Masar, amma duk ba a sami zaman lafiya ba a kasashen. Kuma dukansu kasashe ne wadanda da suke karkashin taron Soviet. Suna gani kamar kasashen dake cikin wannan kungiyar ne a da, ake bi ana yiwa wannan alhali kuwa akwai wadansu kasashen da ba a kulawa da abinda suke yi, suna da sarauta da ba irinta damokaradiya ba amma ba a taba su.
Dalili na karshe da yake yiwa yasa Rasha bata goyon bayan kaiwa Syria hari bisa ga cewar Frofesa shine, suna gani kamar ana kare Isra’ila ne kuma ana neman a raunana kasashen Labarawa ne domin Isra’ila ta bunkasa.