Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kirsimeti: CBN Ya Sahalewa ‘Yan Canji Sayen Dala 25, 000 A Mako Guda


Dalar Amurka
Dalar Amurka

Tsarin zai yi aiki ne a tsakanin 19 ga watan Disamban 2024, zuwa 30 ga watan Janairun 2025.

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bada sahalewar wucin gadi ga masu sana’ar canjin kudade, su sayi abinda ya kai dala 25, 000 a mako guda daga kasuwar hannayen jarin kasar, tsarin da aka kaddamar a farkon watan da muke ciki.

Tsarin zai yi aiki ne a tsakanin 19 ga watan Disamban 2024, zuwa 30 ga watan Janairun 2025.

Sanarwar mai dauke da kwana wata 19 ga watan Disamban 2024, da sa hannun T. G Allu, a madadin mai rikon mukamin daraktan sashen kasuwanci da musayar kudade na CBN, ya bayyana cewa an tsara matakin ne domin biyan bukatar musayar kudaden ketare a lokacin hutu.

Sanarwar ta kara da cewa hada-hadar za ta gudana ne akan mizanin musayar da CBN ya tsayar ta NFEM, kuma za’a bukaci masu sana’ar musayar kudaden su tsaya a kan ribar da bata zarta kaso 1 cikin 100 ba wajen sayar da kudaden musayar ga masu bukata.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG