Watanni goma ke nan da kammala taron tattalin arziki a shiyar arewa maso gabashin Najeriya, taron da gwamnatoci a shiyar suka ce sun yi ne da niyar tattauna hanyoyin shawo kan matsalolin tsaro da suka addabi yankin.
Kwararru a fannonin rayuwa da–ban-da-ban sun bada shawarwari akan inganta sana’ar noma, samar ma matasa da mata ayyukan yi wanda a cewarsu hakan shine zai rage matsalolin tsaro a yankin.
Babban abinda ya fi daukar hankalin mahalarta taron na kwana biyu da aka yi a jihar Gombe shine albishir din da Gwamnan babban Bankin Najeriya a lokacin, wanda yanzu shine sarkin Kano Malam Sunusi Lamido Sunusi yayi. Cewa gwamnatin tarayya a shirye take ta tallafawa duk wata jiha da zata bada lamuni na kafa Bankin Al’umma.
Sa’adatu Mohammed Fawu, wakiliyar muryar Amurka ta tuntubi shugaban kwamitin wanda gwamnatin jihar ta dora ma alhakin ganin an kafa wadannan Bankunan, Alhaji Mohammed Damji, da ta ziyarci ofishinsa, ya fada mata cewa lallai jihar Gombe ta cika fom ta kuma bi duk wasu ka’idodi da ake bukata, ya kuma bayyana mata cewa a shekar 2011, an yi rijistar irin wadannan bankunan kusan sama da 5,000 a Najeriya amma guda 4 ne kawai a jihar Gombe. Ganin muhimmancin wadannan bankunan ne yasa Gwamna (Alhaji Sunusi Lamido Sunusi) ya ga ya kamata a taimaka. Yanzu haka dai an kafa bankunana guda sha daya a jihar.
Malam Damji ya kara da cewa babban Bankin Najeriya na sa ido sosai akan wadannan bankunan haka kuma jihar zata kafa cibiyoyi da zasu kula da harkokin wadannan Bankuna don kada su durkushe.
“wadanna Bankunan zasu taimako ta wajen rage matsalolin tsaro, muddin mutane sun sami karatu na kwarai, da ayyukan yi don kula da iyalansu, saboda za a samar da ayyukanyi ga jama’a” inji Malam Damji.
Ga wakiliyar murya amurka Sa’adatu Mohammed Fawu da karin bayani.