Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sakataren Harkokin Wajen Amurka John Kerry Zai Kai Ziyara Gabas ta Tsakiya a Farkon Sabuwar Shekara


Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry.
Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry.

A wani yunkurin kara karfafa shawarwarin wanzarda zaman lafiya tsakanin Isra’ila da yankin Falasdinu, sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry zai yi tattaki a farkon watan sabuwar shekara zuwa gabas ta tsakiya

Ana sa ran sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry zai fara sabuwar shekara da kai ziyara yankin Gabas ta tsakiya, a wani yunkurin kara karfafa shawarwarin wanzarda zaman lafiya tsakanin Isra’ila da yankin Falasdinu.

A jiya Asabar kakakin ma'aikatar harkoin wajen Amurka Jen Psaki, ta bayyana haka a cikin wata sanarwa d a ta bayar.

Ranar daya ga wata Kerry zai tashi zuwa birnin kudus inda zai gana da PM Benjamin Netanyahu. Daga bisani ya wuce zuwa birnin Ramalla inda zai gana da shugaban yankin Falasdinu Mahmud Abbas. A ganawar da zasu yi, Psaki tace zasu yi magana kan batun yarjejeniyar ta karshe da sassan biyu suke tattaunawa, da kuma wasu batutuwa.

A dai dai lokacinda ake samun labarin ziyarar da sakatare Kerry zai kai yankin, sai aka ji cewa Isra’ila tana shirin sako karin fursinoni ‘yan Falasdinu domin dadadawa. Amma a gefe daya kuma Isra’ila zata bada sanarwar shirin gina sabbin gidaje a sassa da Falasdinawa suka ce nasu ne.

Shugaba Abbas yayi kira ga Amurka ta hana Isra’ila ci gaba da sabon shirin gine ginen, yana gargadin cewa yin haka yana iya wargaza kokarinda Amurka take yi na samun zaman lafiya a yankin.

Babban jakadan na Amurka yana matsawa wajen ganin sassan biyu sun cimma daftari kan yarjejeniya gabannin kurewar wa’adi da aka tsayar na yin haka a wajajen karshen watan Afrilu.
XS
SM
MD
LG