Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jamus Da Brazil Zasu Gabatar Da Kuduri Kan Leken Asiri


Kudurin, zai nemi kare 'yancin mutane na yin magana a waya ko aikewa da sako ta Intanet ba tare da wani ya saci ji ko gani ba

Kasashen Jamus da Brazil sun ce su na zana wani daftarin kudurin da zasu gabatarwa da babban zauren taron MDD wanda zai tabbatar da kare ‘yancin mutane na yin amfani da na’urorin sadarwa ba tare da wani ya saci jin abinda suke fada ko suke aikawa ba.

Jami’an diflomasiyya na MDD dake da hannun a wannan yunkuri sun ce jami’an jakadancin Jamus da Brazil sun gana da takwarorinsu na kasashen Turai da Latin Amurka jiya jumma’a domin tattauna wannan kuduri. Kudurin zai nemi fadada Daftarin “yancin Al’umma da na Siyasa ya kunshi harkokin jama’a a kan hanyar sadarwar Intanet ko yanar Gizo, amma kuma ba zai ambaci sunan Amurka ba.

Wannan kudurin zai kasance wanda ba lallai a yi aiki da shi ba, amma kuma ana daukarsa a zaman karin alamar nuna rashin yarda da ayyukan leken asirin da ake zargin Amurka tana gudanarwa.

Wannan matakin ya biyo bayan rahotannin da suka yi ta fitowa na ayyukan leken asirin da ake zargin Amurka da gudanarwa ciki har da satar jin maganganun shugabannin kasashen waje da wasunsu, matakin da ya harzuka kawayen Amurka da dama.

Hukumar Leken Asiri Ta Na’urori ta Amurka, NSA, ita ce ke tsakiyar wannan fusatar a saboda irin ayyukan satar jin maganganu da karanta sakonnin na’urorin da wani tsohon ma’aikacin leken asiri Edward Snowden ya fallasa.

Tsohon mataimakin darektan hukumar leken asirin Amurka ta CIA, Micahel Morrell, ya fada cikin wata hirar telebijin da za a yada gobe lahadi cewa fallasar da Snowden yayi ta ayyukan leken asirin Amurka ita ce mafi muni da aka taba gani a tarihin ayyukan leken asiri na Amurka.

Morrell ya fadawa shirin 60-Minutes na gidan telebijin na CBS cewa abu mafi muni da Snowden ya fallasa shi ne abin nan da ake kira “Bakin Kasafin Kudi” watau bayanin yadda Amurka take kashe kudadenta na ayyukan leken asiri.

Morrell yace Snowden ya jefa Amurkawa cikin karin hatsari a saboda ‘yan ta’adda su na koyon darasi daga irin wadannan takardun fallasa, kuma zasu yi hattara ta yadda wannan kasa ba zata iya samun bayanan da zata iya samu idan ba don an fallasa yadda take tattara bayanan ba.
XS
SM
MD
LG