Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Amurka Obama Ya Kira Jama'ar Afirka Ta Tsakiya Su Kai Zuciya Nesa


Shugaban Amurka Barack Obama
Shugaban Amurka Barack Obama

A kokarin kawo karshen rikicin Afirka Ta Tsakiya Shugaban Amurka Obama ya kira jama'ar kasar da su kai zuciya nesa.

Shugaban Amurka Barack Obama yayi kira ga jama’ar kasar Afirka ta tsakiya da su kai zuciya nesa duk karin tashe tashen hankula da suke fuskanta.

A cikin wani sako da aka dauka kan fefe domin kasar, Mr. Obama ya maida hankali kan mutanen da ya kira “’yan kasar jamhuriyar Afirka ta tsakiya masu daukaka, cewa suna da ikon daukar mataki sabanin tashe tashen hankula da suka kai ga halaka mutane akalla dari hudu a cikin kwanaki biyu a kasar cikin makon jiya.

Haka kuma yayi kira ga gwamnatin wucin gadin kasar ta kama wadanda suke da alhakin halaka tada tarzomar.

Tunda farko a jiya litinin, kakakin ma’aikatar tsaron Amurka ya ce Amurka zata daukin nauyin jigilar sojojin kiyaye zaman lafiya daga kungiyar hada kan kasashen Afirka zuwa jamhruyar Afirka ta tsakiyan, inda tuni sojojin Faransa suke kokarin tsaida tarzomar. Amurka zata yi jigilar sojojin ne daga Burundi makwabciyar JAT.

Sakataren tsaron Amurka Chuck Hagel ya amince da wannan matakin ne bayan d a ministan tsaron Faransa (Jean-Yves Le Drian) ya gabatar da wannan bukata. Mr. Hagel yace Amurka ta hakikance cewa akwai bukatar daukar matakin gaggawa domin kaucewa mummunar bala’I da zata biyo bayan tarzomar.
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG