Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tattalin Arzikin Duniya Zai Murmure A Hankali - Masana


Wani rahoton da kamfinin dillancin labarai na Reuters ya wallafa a yau ya yi nuni da cewa, wani bincike da wasu fitattun masana tattalin arziki su ka fitar a yau Litinin ya gano cewa, a bana, tattalin arzikin duniya zai murmure a hankali.

Rahoton ya kara da cewa za a shiga halin rashin tabbas sakamakon rikice-rikicen da ake fama da su a sassan duniya, sannan, duniya za ta fuskanci barazanar matsin tattalin arziki a dalilin kirkirarriyar basira wato AI.

Akan gudanar da binciken a duk shekara gabanin taron tattalin arziki na manyan kasashen duniya wato World Economic Forum na shekara-shekara wanda kan gudana a birnin Davos na kasar Switzerland.

Binciken, da ayarin fitattun masana tattalin arziki sama da 60 da akan zakulo daga sassan duniya a fannin gwamnati da masu zama da kansu, su kan fito da abinda bincikensu ya gano wanda shugabani da shugabannin kamfanoni ke nazari akansu.

Yau Litinin ne aka fara taron tattalin arzikin manyan kasashen duniyar a Davos.

A ranar Lahadi da ta gabata ne mataimakin shugaban kasar Najeriya Kashim Shettima ya bar Abuja domin halartar taron.

Shettima zai bi sahun sauran shugabannin siyasa da na kasuwanci daga sassan duniya don halartar taron na tsawon mako guda.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG