Tun daga lokacin da aka bude ofishin EFCC a Kaduna farkon wannan shekarar zuwa yanzu hukumar ta samu korafe korafe fiye da 200 kana ta yi nasarar kwato miliyoyin Naira da dubban dalolin Amurka.
Hukumar ta yi nisa da binciken korafe korafe 130 cikin 200. Ta samu N221m da $17,600.
Malam Kamilu Gini mai magana da yawun hukumar a Kaduna ya kara da cewa jihohi biyar ne a karkashinsu kuma kudaden da suka kwato sun hada da na 'yan kasuwa, ma'aikatan gwamnati da dai sauransu.
Kudaden da suka kwato idan akwai shari'a a kansu sai an gama shari'ar su mayarwa mutum, idan na wani ne ko kuma su shiga aljihun gwamnati idan na gwamnati ne.
Dangane da tsarin nan na tona asiri, Malam Kamilu yace shirin yana aiki amma akwai doka da tace idan mutun ya kawo rahoton da bincike ya nuna na karya ne to zasu kama mutumin su hukumtashi.
Akan kudaden da hukumar ta kwato al'ummar Kaduna sun bayyana ra'ayinsu. Wani Malam Mahmud yace a sa kudin inda suka dace domin zasu taimaka kwarai wajen rage sace sacen da a keyi a kasar. Shi ko Aliyu cewa ya yi suna iyakar kokarinsu amma a yi anfani da kudin a kyautatawa talakawa a yi masu aikin jinkai da zasu ji dadi.
Ga rahoton Isah Lawal Ikara da karin bayani.
Facebook Forum